Ka zama daya daga cikin maziyarta Imam Husain a Ranar 1 ga Watan Muharram sanya sunanka anan ama Ziyara a Madadin ka

Labarai

2021-08-08

4444 Ziyara

Mu'assatul Imam Husain  (as) wacce take karkashin kulawa Haramin Imam ,  ta bada sanarwa amincewa ku da ku saka  sunanku da wadanda kake bukata acikin wadan da za'ayiwa ziyarar Imam Husain a ranar daya ga wata  Muharram, don haka daga yau zuwa Ranar laraba 10/8/2021 shine zai zama ranar kullewa  kuma zaka Iya tura sunan ka da na wanda kake bukata hadi da  Abunda kake bukata ta hanya wannan link din namu na Haramin Imam Husain  (as) shiga wannan link din dake kasa don saka sunanka 

https://www.imamhussain.org/hausa/enaba

Daraktan Musa'assan, Walaa al-Saffar, ya ce, za a gudanar da  ziyarar Imam Husaini, (as), a ranar farko ga watan Muharram mai alfarma a madadin masoyan Ahlulbaiti, (as) ga  waɗanda suka sanya sunayensu a filin ziyarar ta amadadin ka na Haramin Imam Husain 

 Ya kara da cewa miliyoyin masoyan Ahlulbaiti, amincin Allah ya tabbata a gare su, yana da wahala su isa haramin Imam Husaini, (as) don gudanar da bukukuwan ziyara da addu’a a wannan babbar rana, musamman ta la’akari da barkewar cutar Corona Virus.

 Ya yi bayanin cewa hukumar rukunin yanar gizon ta samar da wani shiri mai hadewa don tattara sunayen da ke zuwa shafin ziyarar a madadin yin ziyarar da yin addu’a a madadin ku

Sabbin batutuwa

Wanda aka fi kallo

الزيارة الافتراضية

Zai iya sake Baka mamaki